'Zika ce ke sanya jarirai tawayar kwakalwa'

Hakkin mallakar hoto Getty

Cibiyoyin rigakafin cututtuka na Amurka sun tabbatar da cewa cutar Zika ce ke sanya masu juna biyu haihuwar yara masu dan kai, da kuma tawayar kwakwalwa.

An dai kwashe watanni ana tafka mahawara kan ko cutar na da alaƙa da haihuwar yara masu ɗan kai a Brazil.

Darektan cibiyar ta rigakafin cututtuka, Tom Frieden, ya ce babu wata tantama, ƙwayar cutar ta Zika ce ke haddasa haihuwar yara masu ɗan kai.

Cibiyar ta ce har yanzu tana kan bakanta wajen shawartar masu juna biyu da su ƙauracewa tafiye-tafiye zuwa Latin Amurka da Caribbean, a inda ƙwayar cutar ta fi yaɗuwa.