An fitar da sabon bidiyon 'yan matan Chibok

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An sace 'yan matan ne lokacin da suke rubuta jarrabawa

Gidan talabijin na CNN ya samu wani faifan bidiyo mai dauke da hotunan 'yan mata guda 15 da ake kyautata zaton wasu ne daga cikin 'yan mata fiye da 200 da aka sace, a garin Chibok na jihar Borno, a Najeriya.

A ranar 14 ga watan Afrilun 2014 ne dai wasu waɗanda ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne suka sace 'yan matan daga makarantar sakandare ta garin na Chibok.

Kafar yaɗa labaran ta ce a watan Disamba ne ta samu faifan bidiyon daga hannun wani wanda yake kokarin ganin an sasanta tsakanin 'yan kungiyar Boko Haram da gwamnatin Najeriya wajen sakin 'yan matan.

Image caption Makarantar Chibok ke nan bayan sace 'yan matan

A cikin faifan bidiyon dai, ana iya ganin 'yan mata guda 15 sanye da bakaken hijabi, kuma suna jingine da wani gini mai launin ruwan dorawa.

An jiyo kuma wata muryar namiji yana tambayar sunayensu ɗaya bayan ɗaya da kuma wurin da aka sace su.

Kafar yada labaran ta CNN ta ruwaito cewa faifan bidiyon ya ƙare ne da ɗaya daga cikin 'yan matan, a inda take sanar da gwamnati cewa suna nan lafiya tare da miƙa wasu buƙatu da suke son gwamnati ta biya wa 'yan ƙungiyar ta Boko Haram.

Image caption Iyayen 'yan matan da aka sace suna bayyana bakin cikinsu

Ministan yaɗa labarai na Najeriya, Lai Mohamed ya shaidawa CNN cewa sun samu bidiyon kuma suna nazari a kansa.

Rahotan na CNN ya nuna cewa har zuwa watan Disambar shekarar da ta gabata, wasu daga cikin 'yan matan na Chibok suna raye.