Labarin amaryar da ta kubuta daga hannun BH

Image caption Zara John: Sun bamu zabin mu yi aure ko mu zama bayi - sai na zabi na yi aure.

Shekarun Zara 17, kuma labarinta abin tashin hankali ne. Labarin Boko Haram ne da irin cin zarafin da kungiyar ta Boko Haram ke yi wa dubban mutane a arewa maso gabashin Najeriya da kasashen makwabtaka.

Boko Haram ce ta sace Zara kuma sojoji suka cetota, amma kuma a halin yanzu, ta fi so ta koma dajin Sambisa saboda tsangwamar da take fuskanta da a rayuwarta a matsayinta na wadda ta auri dan kungiyar Boko Haram.

Ba ta cikin 'yan matan makarantar Chibok da suka bata, amma kuma kamar wasu dubban mutanen wa ɗanda aka ceto su ko kuma har yanzu suke hannun 'yan ƙUngiyar, tana cikin wani hali na ha'ulai.

Wannan ne karo na farko da ta bayyana wa wani irin halin da ta shiga shekara ɗaya da ta gabata da kuma irin wahalar da take fama da ita har yanzu.

"Sun bamu zaɓi na ko mu yi aure ko mu zama bayi. Ta ce na zaɓi na yi aure.

Rayuwarta ta kasance mai matuƙar wahala da hadarin gaske.

Image caption Zara ta ce ta zama bare a al'ummar ta

Jiragen sojoji sun kai hare-hare a akasarin dajin sambisa inda sansanin sojin yake kuma daga nan ne sojojin suka cetota kuma ta koma ga danginta.

"Matan da ke danginta sun gano cewar tana ɗauke da cikin wata uku," inji kawunta, Mohammad umaru, wanda yayi mana karin bayani a kan labarinta.

"A danginmu wasu mutanen Musulumai ne wasu kuma Kirista ne. Kafin 'yan ƙungiyar Boko Haram su sace ta kirista ce, amma kuma wanda ya aure ta, sai ya musuluntar da ita."

An samu rarrabuwar kawuna a kan yadda za a ɓullowa al'amarin sai suka kaɗa ƙuri'a a kan ko a zubda cikin ko a bar mata.

Waɗanda su ke so a bar mata cikin ne suka yi rinjaye don haka sai aka bar mata cikin ta haifi ɗanta namiji.

"Ya ce sunan mahaifin mijinta Usman, don haka ne aka sakawa yaron suna Usman," inji Muhammad.

Sai aka fara zage zage.

" Mutane suna kirana matar Boko Haram kuma wasu suna kirana mai aikata mugun laifi. Ba sa so na zo kusa da su." Tana fadin haka ne lokacin da hawaye ke zubo mata.

Yanzu tana zama ne a gidansu kawai, saboda tana tsoron ta fita saboda irin cin mutunci da yaran makwabta ke yi mata.

"Ta ce basa son dana. Idan ya yi rashin lafiya babu mai kula da shi.

Image caption Zara ta ce ta fi son tdajin sambisa a kan ta koma gidansu

A makon da ya gabata, Zara tana kwance a waje da danta Usman saboda zafi, sai maciji ya shigo tsakar gidansu ya sare shi har lahira. Yana wata 9.

Akasarin danginta sun yi murna kan mutuwarsa, inda suka ce haka Allah ya so.

Muhammad ya ce, "mun godewa Allah da yaron ya mutu, suka kara da cewar Allah ya amsa addu'arsu."

"A wasu lokutan, ta kan ce tana so ta je makaranta ta zama likita kuma ta taimakawa al'umma, amma kuma wasu lokutan, idan mutane suka zage ta, sai ta ce ta na so ta koma dajin Sambisa.

"A ko da yaushe tana maganar mijinta wanda kwamanda ne a kungiyar 'yan Boko Haram. Ta ce ta na sonsa saboda yana mata kirki kuma tana so ta fara sabuwar rayuwa da shi."

Zai yi wahala ka yi tunanin shiga irin wannan halin, balle mace mai shekara 17.

Muhammad ya ce ba za ta iya jure rayuwa mai wahala da take ciki ba wanda har yasa wata rana ta ce, "za ta yi yin kunar bakin wake."

Ya kara da cewar "Tabas zata yi kunar bakin wake idan har ta samu dama."

Ba a kula ni

Akwai rikicewa a fuskarta da kuma amsoshin da take bayar wa.

"A yanzu tana matukar so ta koma dajin sambisan, amma kuma zata manta? Ta ce, "zan manta da rayuwar da na yi da Boko Haram amma kuma ba nan kusa ba," inji Zara.

Image caption Zara ta ce tana tsoron ta fita waje saboda zaginta da ake yi

Ta ce tana matukar son mijinta duk da dai ta yi amannar cewa sun cusa mata akidarsu. Tana ganin kamar danginta ba sa kula ta kuma al'umma ta na kyamatarta.

Tana cikin halin kunci kuma tana fushi kuma a rikice take.

"Kawunta ya ce, "Ya kamata mutane su san cewa ba yaran ne suka zabawa kansu irin wannan rayuwar ba, amma kuma idan muka cigaba da kyamatarsu a irin halin kuncin da suke ciki za mu iya haifar da wani abu da ya fi Boko Haram girma a gaba."

'An sace 'yan mata da dama kamar Zara kuma ana tsare da wasu da yawa.

Akwai babban tashin hankali da wadanda suke tsammanin wa rabbuka kuma wadanda suka tsira suna cikin bakin ciki.