'Ya 'yanmu ne a bidiyon BH — Iyayen Chibok

Image caption Iyayen 'yan matan Chibok a zanga-zangar cika shekara daya da sace su

Wasu daga cikin iyayen 'yan matan Chibok sun ce 'ya'yansu ne a wani hoton bidiyo da kafar yada labarai ta CNN ta fitar ranar Laraba.

Iyayen wadanda suka bayyana hakan a wajen zanga-zangar tunawa da sace 'yan matan shekaru biyu da suka gabata a Abuja, sun ce ganin wannan bidiyo ya basu kwarin gwiwa cewa lallai yaran suna raye.

Sun yi kira ga gwamnati cewa ta kara zage damtse wajen ganin an ceto yaran nan tunda dai an samu shaidar cewa suna raye.

Daya daga cikin iyayen 'yan matan Esther Yakubu, ta ce "Rayuwa a dajin Sambisa ba abu ne mai sauki ba, amma dai muna nan muna addu'a dare da rana Allah ya fito mana da su."

CNN ta ce a watan Disamba ne ta samu faifan bidiyon daga hannun wani wanda yake kokarin ganin an sasanta tsakanin 'yan kungiyar Boko Haram da gwamnatin Najeriya wajen sakin 'yan matan.

"Maci"
Image caption An hana masu zanga-zanga shiga fadar shugaban kasa

Kungiyar masu fafutukar ganin an ceto 'yan matan Chibok Bring Back Our Girls ce ta jagoranci zanga-zangar da aka yi a babban birnin Najeriya, wadda daruruwan mutane suka halarta.

Masu fafutakar sun rike kyallaye masu dauke da sakonnin da suke so su isar wa gwamnatin Najeriyar wajen ganin an ceto 'yan matan.

Sun kuma ta yin wake-wake da rera takensu, domin isar da sako ga shugaban kasar Muhammadu Buhari.

Sai dai jami'an tsaro sun dakatar da su shiga fadar shugaban kasar saboda dalilai na tsaro.