Chibok: Garin da aka sace 'yan matansa

A daren da aka sace Jummai daga makarantar sakandaren 'yan mata ta garin Chibok, ta kira mahaifinta a waya.

Tana bayan wata motar a-kori-kura tare da sauran sa'anninta 'yan makarantarsu inda 'yan bindigar da suka sace su suke tare da su. Mahaifinta Daniel, ya ce mata ta yi tsalle ta dira daga motar, amma sai layin wayar ya katse.

Ya fita da gudu daga gida domin ya samu wajen da sabis ya fi karfi. Bayan ya sake kiran wayar sai wani mutum ya dauka ya ce masa, "Ka daina kiran wayar nan, mun tafi da ita."

Daga nan Mista Daniel ya fahimci cewa "Lallai sai yadda Allah ya yi da 'yarsa kawai."

Washegari ya yi kokarin sake kiran layin nata, amma sai ya ji shi a kashe.

Duk da cewa wasu iyalan 'yan matan da suka bata sun bamu damar amfani da hotunansu, amma mun boye sunan Jummai da mahaifinta.

Kafin a sace yaran dai garin Chibok na cikin kwanciyar hankali. Mayakan Boko Haram sun sha kai hare-hare kauyukan jihar Borno amma a wancan lokaci garin Chibok ya tsira.

Daniel wanda ke zaune a garin Mbalala da ke kusa da Chibok ya mayar da 'yar tasa makarantar ne a ranar 14 ga watana Afrilu domin fara zana jarrabawarta ta kammala sakandare.

Amma a cikin wannan dare ne, mayakan Boko Haram din suka dirarwa makaranta cikin shirinsu suka kuma sace Jummai tare da sauran abokan karatunta 275.

Image caption Makarantar Chibok
Shakuwar 'ya da uba

'Yar tasa dai bata ko yi kokarin dira daga motar ba, kamar yadda wasu 'yan matan suka kwatanta kuma suka samu sa'ar tserewa.

Amma Mista Daniel bai taba fidda ran cewa 'yar tasa ba za ta dawo ba. Sun shaku matuka.

Ya ce, "Na fi kowa sanin halin 'yata, ta fi sauran 'yan uwanta maza kwazon aiki, kuma tana tiuka babur tamkar wata namiji."

Watannin kadan da suka gabata, Daniel ya yi kokarin sake kiran lambar wayar 'yarsa.

Sai wani mutum ya dauka ya ce, "Wannan wayar matata ce, me kake nema?"

Mista Daniel ya amsa masa cewa, "Wane ne kai?" Sai shi ma mutumin ya ce, "Kai ma wane ne?" Sai Daniel ya katse kiran.

Kwanaki kadan bayan nan ya sake kiran layin, mutumin ne dai ya sake dauka.

Sai ya ce masa, "Wai me yasa ka ke kiran wayar nan ne?"

Sai Daniel ya yi karya cewa, "Ina kiranka ne saboda na sanka a Maiduguri."

"Idan ka sanni da ba zaka kira ni a layin nan ba," in ji mutumin. Ya ce sunansa Amir Abdullahi, kuma ya ce shi jagoran kungiyar mayakan sa kai ne.

Daga wannan rana Daniel bai sake kiran wayar ba.

Garin da ya zama kufayi

Jummai ta fito ne daga garin Mbalala, mai nisan kilomita 11 daga kudancin garin Chibok, garin da ke cikin wadanda aka sace mutane da dama. 'Yan mata 25 aka sace daga garin Mbalala kawai.

Garin da a baya yake cike da hada-hadar kasuwanci, inda 'yan kasuwa ke zuwa har birnin Kano domin yin sari, a yanzu kam fayau yake kamar an share, duk shagunan a rufe suke. Amma har yanzu rumfunan na nan a kafe a kasuwar duk da cewa ba a cinikayya.

A yanzu dai sojoji sun takaita duk wani al'amari da mutane ke gudanarwa a garin, ba za su iya sayen kayan abinci da yawa ba, kuma ba a kunna janareto da daddare, don haka cikin duhu jama'ar garin ke zama duk dare.

Da yake yanzu ba aikin yi kuma duk makarantu suna rufe, to da wuya ka ga matasa a garin, su kan koma wasu wuraren in har suna da halin yin hakan.

Maza na tafiya wasu garuruwa neman aiki, yayin da ake aurar da 'yan mata da zarar akwai halin hakan

Manyan mata kuwa na kokarin ganin sun kama sana'ar cikin gida ne domin rufin asirinsu, suna sayarwa a bakin hanya.

Maryam Abubakar

A duk lokacin da ake hutun makaranta, Maryam Abubakar kan taimakawa mahaifiyarta wajen sayar da kosai da taliya. A ranar da aka sace Maryam ma kafin ta wuce makarantar, ta taimakawa mahaifiyarta sayar da kayan sana'arta.

Mahaifiyarta ta ce, "Ta yi cinikin wajen dala 50 a ranar, kimanin dubu 15, ta iya kasuwanci sosai. A gona dai bata wani abin kirki, amma wajen sana'a kam zakakura ce sosai."

Wannan ne abu na karshe da ya faru tsakanin 'ya da uwa.

Hansatu Abubakar

Babbar kawar Maryam ita ce Hansatu wadda kuma kanwarta ce da suke uba daya. Tare suke komai, kaya iri daya suke sawa kuma kawayensu ma duk daya ne.

Hansatu na son kayan kawa kuma tana son ta zama mai dinka kayan kawa. Kwanaki kadan kafin a sace su, ta roki mahaifiyarta ta saya mata keken dinki.

Bayan batanta kannenta kan tambaya a duk lokacin da suka ga kayanta wai ina ta tafi ne,kuma yaushe za ta dawo. A karshe dai dole mahaifiyarta ta tattara kayan waje daya ta boye su domin su daina damunta da tambaya.

Ta nuna mana kayan da Hansatu ta tanada domin ta yi amfani da su ranar bikin kawarta, wanda aka sa ranar yinsa kwanaki kadan bayan sun kammala jarrabawar kammala makaranta, bikin da ba a yi ba kenan har yau.

Mahaifiyar tata ta ce, "Zan yi ta ajiye kayan nan har sai ranar da Allah ya dawo da su gida."

Abin tunawa da 'ya'yansu

Wadannan kayayyaki sune kadai abubuwan da suka rage da iyayen yaran ke tunawa da su. Tun bayan da aka dauke 'ya'yansu ba su samu bayani daga gwamnati ba ko sau daya kan inda yaran suke.

Gwamnatin da ta gabata ta ki sauraron iyayen yaran a wancan lokaci, kuma ko ita ma sabuwar gwamnatin bata tabuka wani abin kirki ba domin ceto yaran. Gaskiyar magana ita cebabu wanda ya san inda yaran suke.

Grace Paul

Ga iyayen Grace Paul kuwa, hoto daya ne ya rage musu da suke debe kewar rashin 'yarsu da shi.

Zuwa yanzu dai Grace ta kai shekara 19. Tana son wake-wake, a cewar mahaifinta. Tana son fannin lissafi kuma tana son zama likita.

Bisa amana iyayenta sun bai wa makwabcinsu Aboku Samson hotonta da ya rage domin ya wanko musu katuna da dama

'Yan matan na Chibok dai sune wakilan matasan 'yan mata da dama a kauyen da suka ci burin zama ababen misali ta fuskar cigaba a al'umma.

Sune 'yan mata kalilan da ke kokarin neman ilimi a kasar da rabin matasanta ne kawai ke samun ikon kammala karatun sakandare. A hakan ma gashi wasu sun shiga wani hali.

Aisha Greman

An sace Aisha Greman lokacin da take 'yar shekara 17. Mahaifinta ya ce ta ki yarda ta yi aure lokacin da take makaranta, duk da shi ya so haka din. Tana da kwazo kwarai kuma ta so ta je jami'a domin ta zama kwararriyar ma'aikaciyar lafiya.

Jinkai Yama

Jinkai Yama ita ce babba a gidansu, tana kuma da kanne uku mata. Ta so matuka ta zama soja kuma tana daga cikin kungiyar 'yan sikawut na garinsu.

Kannenta na yawan tambayar ina take. Lokacin da aka samu wata yarinya a watan da ya gabata a Kamaru, kuma aka ce 'yar Chibok ce, duk sun sa rai cewa ita ce.

Amma sai aka gano ashe yarinyar 'yar garin Bama ce, wani gari da ke nesa da Chibok.

A duk lokacin da dare ya yi ko ake ruwa, mahaifin Jinkai kan rufe idonsa yana tunanin ko ina 'yarsa take? Kamar dai sauran iyayen da ke garin, shi ma ya kusa fidda rai da ganinta.

Shi da matarsa basu yarda cewa gwamnati na yin wani kokari don gano su ba.

Mahaifiyarta ta ce, "Idan da suna wani abu da tuni sun aika tawaga zuwa Kamaru."

Shi kuwa mahaifin Jummai ya yi amanna cewar lambar wayar 'yarsa ne zai iya nuna inda take, amma yana tunanin ba wani taimako da gwamnati za ta iya yi masa. Ya ki bayar da nambar wayar tata.

Sintiri

Sojoji kan zo Mbalala lokaci-lokaci, amma kowacce ranar Lahadi su kan wuce masu saide-saide a kasuwa.

Garin dai kusan ba a gudanar da wasu harkoki a yanzu bayan hare-haren kunar bakin wake.

Suna tsoron ganin taron mutane ko ya yake.

Lokacin da muka kai ziyara sojoji sun shaida mana cewa mu dinga lura don kuwa kowa na iya zama dan kunar bakin wake. Wato suna nufin har mata kenan.

Shekaru biyu da suka gabata 'yan Boko Haram suka fara amfani da mata wajen kai hare-haren kunar bakin wake.

Sun kai hare-hare sansanonin 'yan gudun hijira da dama da kasuwanni a wannan yankin. A watan Fabrairu ne suka kai hari kasuwar garin Chibok inda mutane 13 suka mutu.

Wannan al'amari dai bai tsallake iyayen garin Chibok ba, duk da cewa zai yi wuya su yarda cewa ko da 'ya'yansu ake amfani.

Wata uwa ta gaya mana yadda take ji kan wannan zargi, cewa za a iya amfani da 'yarta don kai kunar bakin wake. Ta ce, "Ni fa na haifi 'yar nan, don haka ko da za ta zo da bindiga a hannunta ta ce za ta kashe ni, to ba abin da zai hana na yi mata maraba."

Kungiyar Boko Haram a takaice:
Hakkin mallakar hoto AFP

Kungiyar ta fara ne a shekarar 2002, inda take sukar karatun zamani, wato Boko Haramun ne.

Sun fara kai hare-hare a shekarar 2009

An kashe dubban mutane mafi yawa a arewa maso gabashin Najeriya, an sace daruruwan mutane da suka hada da 'yan makarantar Chibok 200

Sun sanar da shiga kungiyar masu da'awar jihadi ta IS, inda suka ce sabon sunanta shi ne, "IS a yammacin Afrika."

Sun kwace ikon yankuna da dama a arewa maso gabashin kasar, inda suka mayar da su daular musulunci.

Dakarun kawance na yankin tafkin Chadi sun kwato mafi yawan yankunan a bara