Japan: Mutune tara sun mutu a girgizar kasa

Ana cigaba da aikin ceto tun cikin tsakar dare, bayan wata girgizar kasa mai karfi da ta abku a tsibirin Kyushu da ke kudancin kasar Japan.

Girgizar kasar ta rugurguza gidaje, kana akwai rahotannin cewa mutane da dama sun makale a cikin buraguzan gine-gine.

Mutane akalla tara ne suka mutu, yayin da daruruwa ke kwance a asibiti.

Gidan talabijin na kasar ta Japan ya nuna hotunan mutane da suka lulluba da barguna suna tsoron komawa cikin gidajensu.

Dubannin mutane ne ke zaune babu wutar lantarki a garin Mashiki, da ke kusa inda girgizar kasar ta abku.