An tuhumi wata da batancin addini a Kuwait

Hakkin mallakar hoto kuwait.mfa.ir

Wata malamar makaranta mai fafutukar kare hakkin dan Adam a KuwaiT, na fuskantar tuhuma bisa aikata laifin batanci ga addini, a wata hira da ta yi ta talabijin.

An bukaci matar, Sheihka al-Jassem ta bayyana yau a ofishin mai shigar da kara na gwamnati, bayan koken da aka gabatar akan ta, bisa kalaman da ta yi cewa, ya kamata kundin tsarin mulkin Kuwait ya zama yana sama da al'kur'ani da shari'ar musulunci, a al'amuran shugabancin kasar.

Mai shigar da karar na gwamnati ne ke da ikon yanke hukunci ko matar zata fuskanci shari'a ko akasin haka.

Sheikha Al-Jassem, farfesa ce a ilimin Falsafa a jami'ar Kuwait, kuma ana ta samun kiraye-kirayen ganin an kore ta a a jami'ar.