Zimbabwe: Zanga-zanga kan tabarbarewar tattalin arziki

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masu zanga-zangar na bukatar shugaba Robert Mugabe ya sauka daga mulki

Magoya bayan bangaren adawa kimanin dubu biyu ne suka yi zanga-zanga a Harare babban birnin Zimbabwe, domin nuna damuwarsu kan tabarbarewar tattalin arzikin kasar.

Shugaban jam'iyyar Movement for Democratic Change, Morgan Tsvangirai ne ya jagoranci zanga-zangar.

Wasu daga cikin masu zanga-zangar sun rika daga alluna da aka yi rubuce-rubucen kira ga shugaban kasar Robert Mugabe mai shekaru 92, ya sauka daga mulki.

'Yan sandan kwantar da tarzoma sun rufe babbar hanyar zuwa majalisar dokokin kasar.