Apple ya daina kera QuickTime na Windows

Hakkin mallakar hoto Apple

Kamfanin Apple ya dakatar da kera manhajar Quick Time media player ga Windows kamar yadda kwararru a bangaren tsaro suka sanar.

Shafin yanar gizo na Zero Day Initiative wato ZDI ya sanar da cewa an fahimci cewa manhajar Windows tana samun rauni idan ta dauki QuickTime.

To sai dai ZDI ya furta cewa shawara ita ce samar da Windows da tuni aka kera ba tare da yin amfani da irin wanan manhajar ba.

Har yanzu dai kamfanin na Apple bai fito ba a hukumance ya sanar da cewa ya dakatar da samar da QuickTime ga Windows ba.

Apple dai ya yi manhajar QuickTime ce domin kawar da matsalar bidiyo da sauti a kamputa.

A shekara ta 1991 ne aka fito da wanan manhaja a karon farko.