Majalisar Brazil na muhawara kan tsige Dilma

Majalisar dokokin Brazil na tattauna batun tsige shugaba Dilma Rousseff, kafin kuri'ar da za a kada kan lamarin a ranar Lahadi.

Idan har kashi biyu cikin uku na 'yan majalisar suka goyi bayan a tsigeta, to hakan zai hura wutar batun a tsigeta a majalisar dattawa tun kafin ma a gabatar da batun a hukumance.

Kafofin yada labaran kasar na hasashen cewa sakamakon zaben zai yi zafi, ganin yadda Miguel Reale Junior, ya shigar da zazzafar takardar tsige shugaba Dilma Rousseff din, bisa zarginta da boye faduwar da tattalin arzikin kasar ke yi.

To amma babban lauyan kasar, Jose Eduardo Cardoza, ya ce tsigeta tamkar yaki ne da dimokradiyar Brazil.