Cigaban kasa ne ya kai ni China — Buhari

Hakkin mallakar hoto Garba Shehu
Image caption Buhari ya gana da shugabanni da jami'an gwamnatin China

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya ce neman ayyukan raya ƙasa ne ya kai shi ƙasar China.

Ya ce yana son farfado da wasu yarjejeniyoni na ayyukan raya kasa a Najeriya da gwamnatocin da suka wuce suka yi biris da su.

Buhari ya ce ya je Chinan ne domin ci gaba da tattaunawa kan wasu yarjeniyoyi da shugabannin baya suka fara da ƙasar.

Ya ƙara da cewa Najeriya da China sun rattaba hannu a kan wasu yarjeniyoyi da suka haɗa da gina titunan jirgin ƙasa daga Kano zuwa Legas da kuma Legas zuwa Calabar da gina tashar samar da wutar lantarki da kuma harkokin noma.

A hira da yayi da Bilkisu Babangida, yayin kammala ziyarar a China, shugaba Buhari ya ce yarjejeniyoyi na shinfida layin dogo daga Kano zuwa Maiduguri, da aikin madatsar ruwa ta Mambila, an yi biris da su shekara da shekaru.

Ya ce kudaden da China za ta bai wa Najeriya bashi, rance ne mai sauki da za- a biya cikin shekaru 20 masu zuwa.

Shugaba Buharin dai ya fara ne da shaida wa Bilkisun dalilin ziyarar ta sa China:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

A ranar Juma'a ne dai shugaban yake karkare ziyarar tasa.

A ranar Lahadin da ta gabata ne dai Muhammadu Buhari ya tashi zuwa ƙasar ta China tare da muƙarraban gwamnati da 'yan kasuwa.