Akwai yiwuwar kai hari Ghana

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A watan Maris ne aka kai hari kasar Ivory Coast

Hukumar tsaron Ghana ta tabbatar da cewa akwai yiyuwar kai harin ta'addanci cikin kasar.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hukumar tsaron ta rarraba wa manyan kwamandojin hukumar shige da fice, da kuma sauran hukumomin tsaron kasar.

Hukumar tsaron ta ce binciken da ta gudanar tare da wasu bayanai da ta samu, sun nuna cewa bayan harin ta'addancin da aka kai Ivory Coast, Ghana ita ce ta gaba da kungiyar Al-Qa'ida take shirin kai wa hari a nan kusa.

A watan Maris din da ya gabata ne kungiyar Al-Qa'ida ta dauki alhakin harin da aka kai otal din Grand Bassam da ke kusa da wani wajen shakatawa a gabar kogin Ivory Coast.