Girgizar kasa ta sake faruwa a Japan

Hakkin mallakar hoto REUTERSKyodo
Image caption Ana cigaba da aikin ceto a yankin na Kumamoto.

Wata babbar girgizar kasa ta sake afkuwa a birnin Kumamoto da ke Japan, kwana daya bayan faruwar makamancinta da ta yi sanadiyar mutuwar a kalla mutane tara a daidai wannan yankin.

Girgizar kasar da ta kai girman 7.1, ta faru ne da asubahi, inda wasu rahotannin ke cewa an samu kananan girgizar kasar a wasu wuraren ma.

Jami'ai sun yi gargadin cewa akwai yiwuwar afkuwar girgizar kasa a tsibirin Kyushu da igiyoyin ruwa da zasu kai kimanin mita daya.

Ana cigaba da aikin ceto a wannan yanki.