Klopp ya bai wa masu kokwanto mamaki

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jurgen Klopp kocin kulub din Liverpool

Kulub din Liverpool ya ci wasan da za a dade ana magana a kansa a karawar da suka yi da Borussia Dortmund a wasan gasan dab da na kusa da na karshe na gasar Europa.

Ana ganin wannan wasa dai a matsayin wanda za a dade ba a manta da shi ba.

Masu kallo sun ji dadi, an yi hayaniya da kuma nishadi, saboda kyan da wasan ya yi.

Kuma duk wannan ya zo ne kafin dan wasan Liverpool Dejan Lovren ya samu nasarar cin 4-3 a karin lokacin da aka yi daf da tashi wasan.