Microsoft ya yi ƙarar Amurka

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kamfanin dai yana son kotu ta ba wa abokan cinikayyarsa damar sanin neman bayanan sirrinsu

Kamfanin Microsoft ya yi ƙarar gwamnatin Amurka kan 'yancin da kamfanin yake da shi na sanar da abokan hulɗarsa duk lokacin da ya kamata hukumomin gwamnati su karɓi bayanansu na sirri.

Kamfanin ya ce kin bayyana bukatar ta saɓawa kundin tsarin mulkin Amurka.

Tsarin mulkin kasar dai ya fayyace cewa ya kamata kowane mutum ya zama yana da masaniya, a duk lokacin da gwamnati take bincike ko kuma ta ƙwace kayansa.

Microsoft ya ce an miƙa bukatar neman bayanai har guda 5,624, a iya tsawon watanni 18.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wayar komai da ruwanka ta kamfanin Microsoft

Sai dai kuma kamfanin ya ce fiye da rabin bukatun sun zo tare da takardun sammacin kotu da ke neman tilasta kamfanin ya ɓoye bukatar neman bayanan jama'a da hukumomin suka yi.

A cikin shari'ar da kamfanin ya shigar, Microsoft ya ce " mutane ba sa wofantar da 'yancinsu na rike bayanansu na sirri."

Kamfanin na Microsoft ya ƙara da cewa yana kyautata zaton cewa gwamnati " tana son yin amfani da damar amfani da rumbun ajiyar bayanai na Cloud, domin yin amfani da ƙarfin mulki wajen binciken mutane."

Har yanzu dai sashen shari'a na Amurkar bai ce komai ba.