Iyayen 'yan Chibok sun bukaci ayi sabon bincike

Iyayen 'yan matan Chibok sun bukaci gwamnatin Najeriya ta gudanar da sabon bincike kan wasu abubuwa da suka faru gabannin sace 'yan mata 219 da Boko Haram ta yi shekaru biyu da suka wuce.

Iyayen sun yi zargin cewa wasu ma'aikatan makarantar ciki har da masu gadi sun kauracewa makarantar a daren da lamarin ya faru kuma wasu iyayen sun tura an dauko musu 'ya'yansu dake makarantar.

Mr. Yakubu Nkeki shugaban kungiyar wadanda aka sace wa 'ya'ya, a lokacin da ya ke jawabi ga tawagar da shugaban kasar ya tura zuwa garin na Chibok domin jajanta musu, ya ce abin na daure musu kai har yanzu ganin yadda aka bar 'yan matan su kadai a makarantar a daren da aka sace su.

Ministar Kula da muhalli Amina Muhammad wadda ta gabatar da sakon shugaban kasar ga iyayen yaran, ta ce lalle gwamnati za ta binciki wannan lamarin, ta kuma fito da rahoton kwamitin binciken da tsohon shugaba Goodluck Jonathan ya kafa kan sace 'yan matan.