Nigeria na asarar biliyoyi kan rikicin manoma da makiyaya

Wani bincike da wata kungiyar jin kan bil Adama ta kasa da kasa mai suna Mercy Corps ta gudanar, ya nuna cewa ana hasarar kudaden shiga kimanin dalar Amurka muliyan dubu goma sha hudu a duk shekara, sanadiyar rikice-rikice tsakanin manoma da makiya a arewa ta tsakiyar Nijeriya.

Kungiyar dake samun tallafin ma'aikatar raya kasashen waje ta Birtaniya, ta bayyana cewa wajibi ne a yi kokarin dakile wannan matsi.

A cewar Alhaji Haruna Boro Hussaini, tsohon shugaban ƙungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah a jihar Filato dake arewa ta tsakiya, zaman teburin shawarwari tsakanin manoman da makiya akai-akai tsakani da Allah, domin fahimtar matsalolin juna zai taimaka sosai wajen magance matsalar rigingimun.

Baya ga asarar dimbin dukiya, rigingimun na manoma da makiyaya a Nijeriya dai kan kuma janyo hasarar dimbin rayuka da jikkata, inda ko a wannan mako, rahotanni suka nuna cewa mutane kimanin hamsin en suka rasa rayukansu kan sabo da irin wannan matsala a jihar Taraba.