An kama dan Jarida a Bangladesh

Hakkin mallakar hoto focus bangla
Image caption Sheikh Hasina

Jam'iyyar adawa ta Nationalist Party a Bangladesh ta yi alawadai da kama shahararren dan jaridar nan Shafik Rehman, inda ta yi barazanar mayar da kakkausan martani muddin ba a sake shi ba.

An dai tsare shi a Dhaka a ranar asabar da safe bisa tuhumarsa da kokarin sacewa tare da kashe dan firaminista Sheikh Hasina.

Mr Rehman dai shi ne mai bawa shugaban jam'iyyar Khaleda Zia shawara.

Kama shi yakasance na baya-bayan nan a cikin jerin kama 'yan jaridar da aka yi wadanda ke goyon bayan 'yan adawa a kasar ta Bangladesh.