An buɗe hanyar Damaturu zuwa Biu

Hakkin mallakar hoto nigeria defence forces

Shekaru uku bayan rufe ta sojojin Nigeria sun buɗe babbar hanyar Damaturu zuwa Biu a jihohin Yobe da Borno.

An rufe hanyar saboda rikicin Boko Haram da ya tilastawa mazauna garuruwa da dama dake kan hanyar yin gudun hijira.

Buɗe hanyar ya bada dama ga mutane suka koma gidajensu a garin Buni Yadi, wanda 'yan Boko Haram suka taɓa ƙwacewa.

Babban hafsan sojan ƙasa, Laftanar Janar Tukur Buratai ya ce, an bude hanyar ce saboda ingantar sha'anin tsaro.

Hanyar dai ta na da muhimmanci ga tattalin arzikin yankin da ya haɗa jihohin Yobe da Borno, da kuma Adamawa.