Gambia: 'Yan adawa sun zargi gwamnati

Hakkin mallakar hoto AFP

'Yan adawa a Gambia da kuma kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty sun ce, mai fafutukar nan Solo Sandeng ya mutu ne a tsare, bayan kama shi da aka yi yayin zanga-zangar lumana ranar Alhamis.

Amma minista a gwamnatin kasar Sheriff Bojang ya fadawa BBC cewa, ba zai iya tabbatar da ikirarin 'yan adawar ba.

Jiya Asabar 'yan adawa da masu fafutika suka gudanar da zanga-zangar neman a sako duk wadanda aka kama.

Amma gwamnati ta ce, an kama 'yan adawar ne saboda sun yi zanga-zanga ba bisa ka'ida ba.

Ana zargin gwamnatin Yahya Jammeh da gallazawa 'yan adawa.