Ana cigaba da ceto wadanda girgizar kasa ta shafa a Japan

Image caption Masu aikin ceto na namijin kokari wajen ceto mutanen da girgizar kasa ta shafa

Firaministan Japan Shinzo Abe ya bayyana cewa masu aikin ceto na namijin kokari wajen taimakawa wadanda girgizar kasar da aka yi a Japan guda biyu ta shafa.

Mr Abe ya ce dole ne a gaggauta ceto mutanen saboda akwai hasashen da ke nuna cewa za a iya samun afkuwar iska mai karfi da kuma ruwan sama kamar da baki kwarya abinda ke haifar da fargabar samun ruftawar kasa.

Dubban sojoji ne ke taimakawa wajen bincikar baraguzan ginin da ya rufta, inda har yanzu ake neman mutane kusan dari wadanda ba a gansu ba.

Tituna da Gadoji duk sun lalace sakamakon girgizar kasar.

A kalla mutane talatin da biyu aka tabbatar sun rasa rayukansu a girgizar kasar wadda ta kai girman 7.3.