Paparoma zai tafi da wasu 'yan gudun hijra zuwa Italy

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yan gudun hijrar da za su bi Paparoma Francis

Paparoma Francis ya dauki 'yan gudun hijrar Syria musulmai su goma sha biyu zuwa Italy bayan da ya ziyarci wani sansanin 'yan gudun hijra a Girka.

Mutanen wadanda iyalai uku ne sun hadar da yara shida, sun kuma bi Paparoman zuwa filin jirgin saman da ke tsibirin Lesbos domin tafiya tare da shi.

Fadar Vatican ta ce iyalan da Paparoman ya tafi da su sun kasance a sansanin 'yan gudun hijrar kafin a cimma yarjejeniya tsakanin kungiyar tarayyar turai da kuma kasar Turkiyya a kan batun takaita yawan 'yan gudun hijra da ke shiga nahiyar turai.

Fadar ta Vatican ta cigaba da cewa, Paparoman na son ya nuna karamci ne wajen karbar 'yan gudun hijra.

Da ya ke jawabi tun da farko a Lesbos, Paparoman ya bukaci kasashen duniya da su taimaka wajen shawo kan matsalar yan gudun hijrar da ke turai inda ya ce yin hakan dai-dai ya ke da jin kan al'umma.