Sojoji sun kashe fararen hula a Somaliya.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dakarun kiyaye zaman lafiya na tarayyar Afrika

Sojojin kungiyar tarayyar Afrika sun kashe wasu fararen hula hudu lamarin da ya haifar da zanga-zanga.

Daga cikin wadanda aka kashen sun hadar da wata mata mai shekaru tamanin da haihuwa da kuma jikarta 'yar kimanin shekaru tara.

Dukkaninsu ba su da lafiya kuma suna kan hanyar su ne ta zuwa Mogadishu babban birnin kasar ta Somaliya domin neman magani.

Rundunar kiyaye zaman lafiya ta tarayyar Afrika ta ce sojojin wadanda ke cikin yanayi na rudani sun bude wuta ne bayan da motar da ke dauke da mutanen ta ki tsayawa a shingen da aka jiye domin duba ababan hawa.

Wannan lamari dai ya faru ne a gundumar Bulla Marer da ke kudancin kasar.