Girgizar kasa ta kashe mutane 230 a Ecuador

Image caption Masu aikin ceto a wurin girgizar kasa a Ecuador

Ana ci gaba da tura dakaru dubu 10 zuwa arewacin Ecuador, inda akalla mutane 230 suka mutu sakamakon girgizar kasa, wacce ita ce mafi girma da kasar ta taba fuskanta a cikin shekaru masu yawa.

Jirage masu saukar ungulu da motocin bus na jigilar dubban 'yan sanda zuwa yankin.

An rufe manyan hanyoyin mota da dama saboda lalacewar da suka yi.

Magajin garin Pedernales, kusa da inda girgizar kasar ta auku, ya ce gaba dayan garin ya rushe.

Cibiyar nazarin girgizar kasa ta Ecuador ta ce an samu kananan girgizar kasa fiye da 130, bayan girgizar kasar mai karfi da aka samu ranar Asabar.

Shugaba Rafael Correa na kasar, wanda ya katse ziyarar da yake a Italy, ya ce za a samar da dala miliyan 600 domin gyara kayyakin da girgizar kasar ta lalata.