Mutane 41 suka rasu a girgizar kasa ta Japan

Girgizar kasa ta kasar Japan Hakkin mallakar hoto KUMAMOTO PREFECTURAL POLICE
Image caption wani jariri da aka ceto daga karkashin barakuzai

Ma'aikatan ceto a kasar Japan sun kara kaimi a kokarin da suke yi wajen gano wadanda suka tsira a girgizar kasa da ta auku a ranar Alhamis da kuma Juma'a, wadda ta kashe mutane 41.

Har yanzu akwai mutane da dama da suka bata kuma watakila suna makale a karkashin gidagen da suka ruguje.

Ma'aikatan ceto a wasu kauyuka a tsibirin Kyushu sun shafe daren jiya suna hakar kasa duk da cewa an dinga ruwan sama kamar da bakin kwarya.

Wakilin BBC a garin Minami Aso ya ce mutane suna cikin dimuwa kuma ba su taba fuskantar lamari irin wannan ba.