Ma'aikatan mai a Kuwait na yajin aiki

Ma'aikatan man fetur son soma yajin aiki a Kuwait domin nuna fushinsu game da shirin gwamnati na rage musu albashi

Dubban ma'aikatan kamfanin man kasar sun yi ta zanga zanga a wajen hedikwatar kamfanin

Hukumomin gudanarwa na Kamfanin sun ce sun kaddamar da wani shiri na gaggawa domin tabbatar da cewa wannan lamari bai shafi kwastomomi ba.

Kuwait ta fuskanci komabaya a kudaden shiga sakamakon faduwar farashin mai a duniya, sannan wannan shiri da gwamnati ke yi na rage albashin ma'aikata wani bangare ne na irin martanin da gwamnati ke mayarwa dangane da wannan al'amari