An kashe mutane a Zamfara

Hakkin mallakar hoto google
Image caption Gwamnatin jihar ta ce tana daukar matakan kawar da maharan.

Rahotanni daga jihar Zamfara a Nigeria na cewa, wasu mahara da ake zargin Fulani ne sun kashe mutum shida a ƙauyen 'Yar-tsaba.

Wasu mazauna kauyen shun shaida wa BBC cewa lamarin ya faru ne bayan maharan - wadanda suka je kauyen a kan babura - sun buɗe wuta a kan mutanen lokacin da suke gyara gonakinsu.

Yanzu haka dai wasu mutane takwas da harin ya rutsa da su suna jinya a asibitin garin Dansadau.

Jihar Zamfara tana fama da hare-haren da ke haddasa asarar rayuka da dukiya mai yawa.

A baya dai gwamnonin jihohin da ke maƙwabtaka da Zamfara sun yi ta yin tarurruka domin kawo ƙarshen lamarin.