Boko Haram: An yi wa sojin Najeriya kwanton bauna

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sojojin Najeriya sun yi nasarar samun galaba kan kungiyar ta Boko Haram, bayan harin kwanton bauna da suka kai masu ranar Litinin.

Rundunar sojin Najeriya ta ce 'yan kungiyar Boko Haram sun kai hari kan dakarunta na bataliya ta 113 da ke Kareto a arewacin jihar Borno.

Rahotanni daga jihar Bornon sun ce mayakan kungiyar Boko haram sun kai wa sojojin Najeriya harin kwanton bauna a garin Kareto da ke kusa da kan iyakar Najeriya da Nijar.

Sanarwa da kakakin rundunar sojin kasa ta Najeriya, Sani Kukasheka Usman, ya aikewa manema labarai ta ce dakarun na can suna fafatawa da mayakan Boko Haram tun da sanyin safiyar ranar Litinin.

Wata majiya a rundunar sojin kasa ta Najeriya ta ce wasu sojoji sun rasa rayukansu, yayin da kuma wasu suka bata sakamakon harin.

Sai dai wani mazaunin yankin ya shaida wa BBC cewar sojojin Najeriya sun kashe mayakan kungiyar Boko Haram da dama kuma garin Kareto na karkashin ikonsu.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ga karin bayani a rahoton da wakilyar BBC Raliya Zubairu ta hada mana.