Jami'an tsaro 47 sun ɓata a Chadi

Hakkin mallakar hoto

Iyalai da masu fafutikar kare haƙƙin bil'adama a kasar Chadi sun ce dakarun tsaro 47 sun ɓata saboda sun ƙi zaɓen Idriss Deby a zaben shugaban kasar da ya gabata.

Wasu mata biyu sun ce an kama mazansu ne saboda sun zabi dan takara na 'yan adawa.

Tuni Joseph Djimrangar Dadnadji jigo, a ɓangaren adawa, ya yi kiran a sako jami'an tsaron da aka kama.

Amma wani kakakin 'yan sandan Chadi ya shaida wa BBC cewa babu wani ma'aikacinsu da ya salwanta.

Har yanzu ba a fitar da sakamakon zaben shugaban kasar Chadin ba, amma ana kyautata zaton shugaba Idriss Deby ne zai lashe shi.