Girgizar kasa ta kashe mutum 413 a Ecuador

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mutane fiye da 2000 ne suka samu raunuka.

Gwamnatin Ecuador ta ce adadin mutanen da suka mutu sanadiyar girgizar kasar da ta faru a kasar a karshen makon jiya ya kai mutum 413.

Masu aikin agaji sun yi ta yunkurin ceto mutanen da suka makale a baraguzan gine-gine.

Jami'ai daga kasashen Switzerland, da Spain da kasashen Latin Amurka da dama sun je Ecuador domin taimakwa wajen aikin ceto.

Mutane sama da 2,000 suka samu raunuka sakamakon girgizar kasar.

Tun da fari dai, Shugaba Rafael Correa, ya yi gargadin cewa adadin mutanen da suka mutu zai karu, yana mai cewa akwai mutane da dama da gine-gine suka danne.