Litattafai: Google ya yi nasara

Hakkin mallakar hoto Getty

Kotun ƙolin Amurka ta yanke cewa, kamfanin Google zai iya ci gaba da sanya litattafai a shafukansa.

Wannan ya kawo ƙarshen jayayya ta shekaru 11 tsakanin kamfanin na Google da wasu marubuta.

Marubutan suna zargin cewa, sanya litattafan da suka rubuta a shafukan Google ya keta hakkinsu na mallaka.

Amma hukuncin da kotun ƙolin ta yanke akan wannan batu shi ne mataki na ƙarshe.

Google na sanya shafukan da sassan wasu litattafai a shafinsa dake baiwa jama'a damar karantawa.

Su dai marubuta suna ƙorafin cewa, sanya litattafansu a shafukan Google yana kawo koma baya ga irin kuɗaɗen da zasu iya samu.