Nijar: Bangaren adawa zai koma majalisa

Hakkin mallakar hoto Getty

Kawancen jam'iyyun siyasa na bangaren adawa COPA a jumhuriyar Nijar sun janye matakan da suka dauka na kauracewa zaman majalisar dokoki.

Matakin kauracewa majalisar da 'yan majalisar bangaren adawa suka dauka sun yi shi ne domin nuna rashin amincewa da yadda aka gudanar da zaben shugaban kasar.

Sai dai wasu daga cikin magoya bayansu na adawa da matakin komawa majalasar.

'Yan adawar sun kauracewa zaman majalisar ne domin nuna adawa da yadda aka gudanar da zaben shugaban kasar.

Nan gaba dai ne za a gudanar da zaben kankanan hukumoni a kasar ta Nijar.