Matsalar karancin wutar lantarki a Najeriya

Hakkin mallakar hoto bbc

Bisa ga dukkan alamu tsananin matsalar karancin wutar lantarki da ake fama da ita a Najeriya zai ci gaba har zuwa karshen watan gobe.

Gwamnatin kasar dai ta ce ana samun karancin wutar ne sakamakon lalata wasu manyan bututan iskar gas da ke samar da kashi 40 cikin 100 na yawan gas din da tashoshin samar da wutar lantarkin ke amfani da shi.

A yanzu dai ofishin mataimakin shugaban kasar ya ambato kamfanin mai na Shell na cewar gyaran bututan zai kai har karshen watan Mayu.

A Najeriyar dai an shafe dogon lokaci ana fuskantar matsalar wutar lantarki a fadin kasar baki.

Wannan matsala, a ganin wasu, har yanzu ta- ki- ci ta- ki- canyewa.