An bukaci El-Rufai ya soke dokar addini

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption CAN ta ce ƙudurin dokar ya ci karo da 'yancin yin addini ba tare da tsangwama ba.

Ƙungiyar Kiristocin ta CAN a Najeriya ta yi kira ga gwamnatin Kaduna da ta janye ƙudurin dokar da ke neman yin kwaskwarima kan yadda ake yin wa'azi.

A wani taro da ta gudanar a Zaria, CAN ta ce ƙudurin dokar ya ci karo da 'yancin yin addini ba tare da tsangwama ba.

Wasu daga cikin shugabanni da mabiya addinin Kirista a wajen taron sun shaida wa BBC littafin Linjila ya bukace su, su rika yin wa'azi babu dare babu rana, sabanin bukatar da kudirin dokar ya yi cewa a kayyade lokacin yin wa'azi.

Gwamnatin jihar ta Kaduna ta ce tana son kafa wannan doka ce domin katse hanzarin yin wa'azi barkatai, da kuma matsalolin da ke tasowa sanadiyyar hakan.

Sabuwar dokar ta tanadi samun lasisi kafin Malami ya yi wa'azi, kuma ƙa'ida a kan wuraren da za a iya yin wa'azin addini.

A baya dai jihar Kaduna na daga cikin jihohin Najeriya inda rikicin addini ya fi yin ƙamari a arewacin kasar.