'Yan ci ranin Somaliya sun nutse a tekun Bahar Rum

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tururuwar 'yan ci rani Turai ya janyo tsaurara tsaro a kan iyakokin kasashen Turai.

Ana fargabar wani jirgin ruwa dauke da 'yan cira 400, yawancin su kuma 'yan Somaliya, ya nutse bayan kifewar da ya yi a tekun Bahar Rum, kusa da tekun Masar.

Wani babban jami'i a Masar ne ya tabbatar da rahotannin, bayan rubuce-rubuce ta intanet da wasu iyalan wadanda abin ya rutsa da su, sun mamaye kafofin sada zumunta.

Rahotanni sun ce an kai wasu cikin wadanda suka sha da kyar tsibirin Girka.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane 180,000 ne suke yunkurin zuwa turai ta hanyoyin ruwa a duk shekara, inda kusan mutane 800 suka rasa rayukansu.