Tattaunawa a kan Syria na fuskantar barazana

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan tawayen Syria sun kai hari a Latakia

Tattaunawar zaman lafiyar da ake yi a Geneva na fuskantar barazana sakamakon yunkurin da wakilan 'yan dawa ke yi na ficewa daga wajen tattaunawar.

Rahotanni sun ce ana samun barkewar rirkici a wasu wuraren a Syria, inda rahotanni suka ce 'yan tawayen sun kai wa dakarun gwamnati hari a arewa maso yammacin lardin Latakia wanda shi ne ainihin garin shugaba Bashar al-Assad.

Harin ya faru ne bayan da bangaren 'yan adawa a Syrian su kayi gargadin cewa za su kai na su harin saboda bangaren gwamnati sun karya yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma.

Masu sharhi sun ce akwai yiwuwar wutar rikicin da ta ke kara ruruwa za ta kawo cikas a tattaunawar zaman lafiyar da ake yi a Geneva inda ba bu wata alamar amincewa da yarjejeniya.

'Yan adawar dai sun ce za su fice ne saboda ba bu wani abu da aka cimma a wajen tattaunawar ya zuwa yanzu.

Su dai 'yan adawar sun hakikance cewa sai shugaba Bashar al-Assad bya sauka daga mukaminsa.