Zambia: Ana zargin baki da tsafi

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaban kasar Zambiya Edgar Lungu.

A Zambiya, an tura jami'an tsaro wasu yankunan Lusaka, babban birnin kasar, bayan an yi ta wawashe kantunan 'yan kasashen waje sakamakon zargin da ke cewa 'yan kasashen waje na da hannu a kashe-kashen dake da nasaba da tsafi da ake yi a kasar.

Daruruwan mutane ne suka shiga zanga-zangar, inda yawancin shagunan da aka wawashe din na 'yan kasar Rwanda ne.

Ana zargin 'yan kasashen waje tsafi da sassan jikin mutane.

Akalla mutane 6 ne aka ce an kashe a 'yan makwannin bayan nan, inda aka datse wasu sassan jikin nasu kamar kunne da zuciya da sauransu.