Bam ya kashe fiye da mutum 28 a Kabul

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Jami'an tsaro sunyi wa inda aka kai wa hari kawanya

Jami'an tsaro a Afghanistan sun ce mutane fiye da 28 sun mutu, sannan sama da mutane 329 suka jikkata sakamakon wani harin kunar-bakin-wake da aka kai a Kabul, babban birnin kasar.

Rahotanni sun ce wani dan kunar bakin wake ne ya tada bam a cikin wata mota sannan 'yan bindiga su ka mamaye yankin.

Bam din ya fashe ne da sa fe lokacin da mutane ke ruguguwar fitar aiki a wata unguwa da ke kusa da ma'aikatar tsaro da kuma gidajen sojoji.

Kakakin ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar, Sediq Sediqqi, ya ce wani dan kunar-bakin-wake ne ya tayar da bam din a wata mota, kuma ana ci gaba da jin harbin bindiga.

Jami'an tsaro sun ce an kawo karshen harbe-harben kuma an bude hanyoyin da yankin.

Wani mai magana da yawun kungiyar Taliban ya ce kungiyar ce ta kai harin.

Harin dai ya zo ne mako guda bayan kungiyar Taliban din ta ce tana shirin kai munanan hare-hare.