'Yan Boko Haram sun yi wa Kwamandan soji kwanton-bauna

Hakkin mallakar hoto AP

Rundunar sojin Najeriya ta ce mayakan kungiyar Boko Haram sun yi wani mukaddashin kwamandan ta kwanton-bauna ranar Talata.

A wata sanarwa da kakakin rundunar sojin kasa, Kanal Sani Kukasheka Usman, ya fitar ya ce ana zaton 'yan Boko Haram ne suka kai wa tawagar Birgadiya Janar Victor Ezugwu hari, a hanyar su ta zuwa garin Bama, da ke jihar Borno a arewa maso gabashin kasar.

Sanarwar ta ce duk da cewa dakarun sun yi nasarar dakile harin kwanton baunar, soja daya ya rasa ransa, yayin da sojoji biyu suka samu rauni.

A cewar Kanar Kukasheka, dakarunsu sun kwato mota kirar Hilux guda daya da bidigogi samfurin AK-47 guda biyu da makamai da dama a hannun 'yan bindigar.

Mukaddashin kwamandan rundunar sojin dai ya ci gaba niyyar sa ta ziyartar garin na Bama, a yayin da aka karasa da sojan da ya rasu da kuma wadanda suka samu rauni zuwa birnin Maiduguri.

Sanarwar ta kara da cewa Babban hafsan sojojin kasar Laftanan janar Tukur Yusuf Buratai ya yi magana da mukaddashin kwamnadan sojojin.

A ranar Litinin ne Boko haram suka yi wa sojojin Najeriya kwanton-bauna a garin Kareto da ke kusa da kan iyakar Najeriya da Nijar, duk da cewa sojojin sun yi nasarar dakile wannan harin.