Nigeria: Jama'iar Bayero ba za ta bayar da Digirin girmamawa ba

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A baya dai jami'ar ta BUK tana bayar da irin wannan digirin na girmamawa.

Jami'ar Bayero University da ke Birnin Kano na arewacin Najeriya, ta ce ba za ta karrama kowa da digirin girmamawa ba a bikinta na yaye ɗalibai na wannan shekarar.

Mataimakin shugaban jami'ar, Farfesa Yahuza Bello wanda ya shaidawa BBC hakan, ya ce mutum ɗaya ne kawai jami'ar za ta karrama, wato shugaban jami'ar wanda aka fi sani da Chancellor.

Ya ce jami'ar ba za ta karrama mutanen ba ne saboda ƙurewar lokaci wajen yin nazari wajen ware mutanen da suka cancanta.

Farfesa Bello ya ƙara da cewa za su bayar da digirin na girmamawa nan gaba.

Al'adar jami'o'in Najeriya ce karrama hamshaƙan masu kuɗi da 'yan siyasa da sarakai da jami'an gwamnati, da irin wannan digirin na girmamawa.