Dasuki: Kotu ta yi watsi da bukatar gwamnati

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ana zargin Kanar Sambo Dasuki da sace $2.1bn

Wata babbar kotun Najeriya da ke Abuja ta yi watsi da bukatar gwamnatin kasar ta yi wa Kanar Sambo Dasuki, tsohon mai bai wa shugaban kasar shawara kan sha'anin tsaro, shari'a a asirce.

Ita dai gwamnatin tarayyar kasar ta ce tana so a yi shari'ar a asirce ne domin gudun kada shaidun da za ta gabatar a gaban kotun kan zargin da ake yi masa na yin almundahana da kudade, su fuskanci barazanar kisa.

Sai dai alkalin kotun ya ce gwamnatin ba ta gabatar da shaidun da ke nuna cewa idan aka yi shari'ar a fili, hakan zai iya cutar da shaidun ba.

Ana zargin Kanar Dasuki ne da sace kudi kimanin $2.1bn wadanda aka ware domin sayen makaman da za a yi yaki da kungiyar Boko Haram.

Sai dai tsohon mai bai wa tsohon Shugaba Goodluck Jonathan shawarar ya musanta zargin.