Dewalt ya kaddamar da gagarumar wayar salula

Dewalt smartphone Hakkin mallakar hoto Dewalt GMC
Image caption Dewalt smartphone

Kamfanin gine-gine na Dewalt ya kera samfurin wayoyin komai da ruwan ka ''daki bari'' da za su taimaka wa masu aiki a kamfanonin gine-gine.

An kera wayoyin ne ta yadda za su iya jure wa faduwa kan daben siminti daga tsawon mita biyu , kana za a iya amfani da su a yanayin zafi daga ma'aunin ashirin zuwa sittin.

Kasuwar wayoyin da ake kira '' daki bari'' ta samu karbuwa, kamar yadda manajan kamfanin wayoyin salula na Tuffphones James Booker ya shaidawa BBC.

Mr Booker ya kuma ce ma'aikatan kamfanonin gine-gine da masana'antu, har ma da masu sha'awar wasanni, sun gane cewa amfani da jakar saka wayoyin salula masu kauri kadai ba zai taimaka musu ba.

Kana dole sai an yiwa wayoyin salular gwaje-gwaje da suka hada da faduwa a kasa da, kana akwai bukatar wayoyin su kasance suna da kariya daga ruwa da kuma kura kafin a amince da ingancin su.

Samfurin wayoyin salula na Dewalt MD501, sun fito ne da wasu siffofi na ba kasafai ba, kana fuskokinsu an yi su ne da wasu gilasai na musamman, ta yadda za a iya sarrafa su ko da kuwa da safar hannu ce.