Equador: Yawan wadanda suka mutu ya karu

Girgizar kasa a Equador Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Adadin wadanda suka mutu a girgizar kasa a Equador ya karu.

Gwamnatin kasar Equador ta ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon girgizar kasar da aka yi a kasar ranar Asabar ya karu zuwa sama da 500.

Mataimakin ministan harkokin cikin gida, Diego Fuentes wanda ya sanar da hakan ya yi gargadin cewa, alkaluman ka iya karuwa a dai-dai lokacin da masu aikin ceto suka yi kasa a gwiwa wajen samun damar ceton karin wasu mutanen.

Har yanzu dai ba aji duriyar kimanin mutane dubu biyu ba, tun bayan ibtila'in da ya afkawa kasar.

Haka Kuma mutane dubu ashirin girgizar kasar ta haddasawa rasa gidajensu.