Niger: An kulle jami'an gwamnati kan satar jarrabawa

Hakkin mallakar hoto
Image caption Wani mutum ne ya kai karar mutanen.

A Jamhuriyar Nijar, hukumomin shari'a sun tasa keyar wasu mutum goma da suka hada da manyan jami'an gwamnati zuwa gidan kaso, kan badakalar satar jarrabawa.

Kotu na zarginsu ne da aikata laifuka daban-daban cikin jarrabawar daukar ma'aikatan ma'aikatar ilmi da aka fito da sakamakonta a 'yan kwanakin baya-bayan nan.

Sabbin ma'aikata 1831 ne ma'aikatar kwadago ta tantance daga cikin sama da dubu sha hudu da suka yi jarabawar, sai dai gwamnatin ta soke ta saboda magudin da ta ce an tafka.

Wani mutum ne da bai samu nasarar jarrabawar ba ya gabatar da koken sa gaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasar.

Hakan ne ya sa hukumar ta gudanar da bincike inda ta gano cewar akwai alamomi masu karfi da suka tabbatar da an yi cuwa-cuwa a cikin jarrabawar.

Binciken ya gano cewa akwai mutanen da ba su dau jarrabawar ba amma sunayen su ya fito a cikin jerin wadnda suka samu, da dai sauran kura-kurai.