Amurka ta nuna fushinta da Reik Machar

Hakkin mallakar hoto

Amurka ta nuna fushinta kan kin komawar jagoran 'yan tawayen Sudan ta Kudu Reik Machar zuwa Juba babban birnin kasar, a bisa yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimma.

Mai magana da yawun ofishin huddar jakadancin Amurka John Kirby ya ce, matakin na Mr Machar ya saka rayuwar 'yan kasar Sudan ta Kudun cikin hadarin fadawa cikin wani sabon tashin hankalin da kuma fuskantar akuba.

Mr Macahr din dai zai karbi mukaminsa na mataimakin shugaban kasa ne a sabuwar gwamnatin hadin kan kasa, da ke nufin kawo karshen rikicin da aka shafe shekaru biyu ana tafkawa.

Yan tawayen dai sun ce an jinkirta dawowar Mr Machar din ne kan wasu dalilai na harkokin mulki.

Amma kuma gwamnatin ta yi zargin cewa yana son zuwa da makamai ne, wanda ba abinda za a amince bane.