Mutane 40 sun mutu a Syria

Hakkin mallakar hoto Reuters

Rahotanni daga arewa maso yammacin Syria sun ce an kai hare-hare ta sama a wata kasuwar kayan gwari, inda aka kashe tare da raunata mutane da dama.

Rahotannin sun ce an kashe akalla mutane 40 a Ma'arat al-Numan dake Lardin Idlib, inda yawanci ke karkashin ikon 'yan tawaye.

Dakarun gwamnatin Syria da Rasha na ta kai hare hare wuraran da ke hannun 'yan tawaye a yankin.

Wannan harin na zuwa a daidai lokacin da shugaban babbar kungiyar 'yan adawan Syrian dake wajan tattaunawar da ake a Geneva ya ce dakarun gwamnati sun karya yarjejeniyar tsagaita wutar.

A jawabin da ya yi cikin fushi, Riad Hijab ya tabbatar da cewa 'yan adawan za su fice daga tattaunawar, inda ya ce ba za su zauna ba a yayin da jama'a a Syria ke can suna ta mutuwa.