Za a yi wa 'yan Uganda maganin cutar daji kyauta

Hakkin mallakar hoto UCI
Image caption Lalacewar da na'urorin kashe cutar daji na Uganda suka yi ta je dubban masu fama da cutar cikin mummunan hali.

Wani asibitin kasar Kenya ya ce zai yi wa 'yan Uganda masu fama da cutar daji 400 magani kyauta.

Asibitin Jami'ar Aga Khan ya ce zai dauki wannan mataki ne bayan na'urorin kashe kwayoyin cutar daji da ake amfani da su a Uganda sun lalace.

Mahukuntan asibitin sun kara da cewa za su karfafa gwiwar wasu asibitocin su yi wa masu fama da cutar irin wannan magani.

Lalacewar da na'urorin kashe cutar daji na Uganda suka yi ta je dubban masu fama da cutar cikin mummunan hali.

Gwamnatin Uganda ta ce za ta biya kudin jirgi da na abincin mutanen da za su je Uganda domin samun maganin cutar ta daji a birnin Nairobi.

Yin maganin cutar daji na da matukar tsada, kuma akasarin masu fama da cutar a Uganda ba za su iya biyan kudin maganin ba.