Boko Haram na bai wa matasa rancen kudi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sojojin Najeriya su na cigaba da samun nasara kan kungiyar Boko Haram

Shalkwatar tsaron Nigeria ta ce sun gano cewar kungiyar Boko Haram na bai wa matasa rancen kudi domin su ja hankalinsu wajen shiga kungiyar.

Wata sanarwa dauke da sa hannun kakakin Shalkwatar tsaron ta Najeriya Birgediya Janar Rabe Abubakar ta ce kungiyar ta Boko Haram ta samar da wata hanya daban ta jan hankulan matasa, inda ta ke bai wa matasa masu kasuwanci da sana'ar hannu da su ke arewa maso gabas rancen kudi domin su dauke su aiki.

Shalkwatar tsaron ta ce kungiyar na harin matasan da ke arewa maso gabas, musamman mahauta da 'yan kasuwa da masu sana'ar dinki da masu yi wa mutane kwalliya da wasu masu sana'oin hannun wadanda za a iya jan hankalinsu da rance ba tare da sun yi la'akari da haduran da ke tattare da amincewa da tallafin da zai fito daga wurin kungiyar ba.

Bayan sun bayar da bashin, 'yan kungiyar ta Boko haram sai su bawa wadanda suka karba zabin ko dai su shiga kungiyar a yafe musu, ko kuma su biya, idan kuma suka gaza biya a kan lokaci za a kashe su, alhali kuma kungiyar ta yi tsarin da wanda ya karbi bashin ba zai iya biya ba.

A don haka Janar Rabe Abubakar ya bukaci jama'a, da su kaucewa karbar basussuka a cibiyoyin da ba na hukuma ba.

Hukumar tsaron ta ce nasarar da sojojin Najeriya suke cigaba da yi a kan kungiyar ya sa ragowar 'yan kungiyar suka matsu da su dauki wasu mutanen aiki.

Kakakin shalkwatar tsaron ta Najeriya ya shawararci mutanen gari, musamman wadanda su ke arewa maso gabas da su kula kuma su mayar da hankali kan irin sababbin dabarun kungiyar ta Boko Haram don kaucewa fadawa cikin matsalar da za ta kai su ga halaka.