EFCC ta gano ma'aikatan bogi 37,395

Hakkin mallakar hoto efcc
Image caption EFCC ta ce za a cigaba da gano ma'aikatan bogi

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Nigeria zagon-kasa, EFCC ta ce ta gano ma'aikatan gwamnatin tarayya na bogi su dubu 37, 395.

Shugaban hukumar Ibrahim Magu ya ce sun gano wadannan mutanen ne a wani aikin hadin gwiwa da ma'aikatar kudi da kuma ofishin babban Akawun gwamnatin tarayya, yana mai cewa hakan ya sa gwamnatin tarayya ta yi asarar kusan Naira biliyan daya.

A cewar hukumar, za a ci gaba da gano ma'aikatan bogi a yayin da suke ci gaba da bincike a rijistar albashin ma'aikatun gwamnatin tarayya.

A baya dai, ministar kudi, Kemi Adeosun, ta ce an gano dubban ma'aikatan bogi a kasar.