Ghana: Masana'antu na gaf da durkushewa

Hakkin mallakar hoto elvis

A kasar Ghana masana'antun saka zannuwa da ke samar da dubban guraben ayyuka ga ma'aikata na gaf da durkushewa in ji kwararru.

A shekara ta 1980 kasar Ghana na da masana'antun saka zannuwa musamman atamfa guda 20 wandan ke samar da guraban ayuuka dubu talatin da biyar.

Yanzu da al'amura suka sauya masana'antu hudu da suka rage ne kawai ke samar da guraban ayyuka dubu uku kacal.

Hakan na faruwa ne saboda yadda kasuwannin zannuwan da ke cike da zannuwan da aka yi kwaikwayon saka su a kasashen waje musamman kasar China.

A shekara ta 2010 ne gwamnati ta kafa wata tawaga ta musamman da zata rika kwacewa da lalata zannuwa yin Chinar, to amma hakan bai yi tasiri ba.

Sai dai a yanzu gwamnati ta fara daukan matakan magance matsalar, kamar yadda karamin ministan masana'antu ya shaidawa BBC.